Wani fasto kasan Ghana na Domeabra mai suna, Vincent Kete, zai kwashe shekaru 20 a gidan yari da aikin wahala bisa ga laifin fyade wa yar shekara 13.

An yankewa fasto shekara 20 a gidan yari bayan yayi wa ‘yar yarinya fyade
Jaridar 3News ta bada rahoton cewa fasto Kete ya amsa cewa ya aikata wannan laifi. A gurfanar da akayi masa a kotu, lauya Kofi Atimbiri ya tuhumceshi da kiran yarinyan zuw dakinsa a ranan Talata, 7 ga watan Fabrairu, kuma yayi mata fyade.
Faston da mahaifin yarinyan sun kasance abokan juna wanda har daki daya sun zauna a cocinsu. Faston da ya fadawa kotu cewa wannan kaidin shaidani ne kuma shi bai san abinda ya faru da shi ba.
Bayan an sauraresa, kotu ta yanke masa shekaru 20 a gidan yari da aikin wahala.
We appreciate you for reading Teeloadeders, but we think it will be better you like our facebook fanpage and also follow us on twitter below.
Title :
An yankewa fasto shekara 20 a gidan yari bayan yayi wa ‘yar yarinya fyade
Description : Wani fasto kasan Ghana na Domeabra mai suna, Vincent Kete, zai kwashe shekaru 20 a gidan yari da aikin wahala bisa ga laifin fyade wa yar sh...
Rating :
5