- Gwamnatin jihar Sakkwato ta dauka matasa marasa aikin yi fiye da 500 a ma’aikatar muhali na jihar
- Jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar muhalli ya ce dauka matasan aikin watanni biyu da suka wuce
- Abdullahi ya ce irin wannan manufar ita ce na karon farko a cikin tarihi na jihar.
Gwamnatin jihar Sakkwato ta dauka fiye da matasa 550 aikin na duba gari na yau da kullum a jihar a matsayin wani ɓangare na hana ambaliya da kuma bunkasa kiwon lafiyar al’umma.
Majiyar 24repoters.com ta tabbatar da cewar, Malam Abubakar Abdullahi, Jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar muhalli, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba, 26 ga watan Yuli cewa ma'aikatan ta dauki matasan aiki kimanin watanni biyu da suka wuce yayin da aka kuma tura su wurare daban-daban a fadin jihar.
Ya ce an dauki matasan aiki ne don karfafawa su ta fuskar tattalin arziki da kuma hana su zaman kashe wando. Ya ce sabbin ma’aikatan dubagarin za su tamaika wa shirin tsabtace muhalli na wata-wata na gwamantin jihar.
Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal
Abdullahi na mai cewa aikin jadawali na sabbin ma’aikatan dubagari sun hada da share-sharen magudanun ruwa da fitad da shara daga magudanun ruwa da kuma shara tituna da sauran ayyukan da ta shafi tsabtace muhalli..
KU
KARANTA: Mai magana da bakin Shugaban kasa yayi gum game da ranar dawowar Buhari
Abdullahi ya yabawa shirin gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal na samar wa matasa ayyukan yi cewa wannan zai tamakawa matasan. Ya ce wannan manufar ita ce na karon farko a cikin tarihi na jihar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@24reporters.com
We appreciate you for reading Teeloadeders, but we think it will be better you like our facebook fanpage and also follow us on twitter below.
Title :
Sakkwato: Gwamnatin jihar Sakkwato ta ba matasa fiye da 500 aiki a ma’aikatar muhalli na jihar
Description : - Gwamnatin jihar Sakkwato ta dauka matasa marasa aikin yi fiye da 500 a ma’aikatar muhali na jihar - Jami'in hulda da jama'a na ma...
Rating :
5