Wasu karnuka biyu sun dakile yunkurin kai hari da wasu yan kunar bakin wake biyu suka yi a babban asibitin Moloi dake Maiduguri.
Harin da aka dakile shine sabon harin da ‘yan ta’addan Boko Haram dake arewa maso gabashin Najeriya suka kai.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Borno, Mista Fatomi Ahmed, ya tabbatar da al’amarin a wani hira da manema labarai bayan harin.
Ahmed ya ce hukumar ta aika da tawagar masu ceto da su je wajen da harin ya afku.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: El-Rufai, da sauran mambobin kwamitin APC na cikin ganawa mai muhimmanci
Kakakin hukumar tsaro na hadin gwiwa wato CJTF, Malam Bello Danbatta wanda ya tabbatar da al’amarin yace karnukan da yan kunar bakin waken sun mutu a take amma ba’a rasa ran kowa ba.
Wani shaidar gani da ido, Mista Rilwan Isah yace haushin da karnukan biyu ke tayi ne ya hana yan kunar bakin waken samun damar shiga harabar asibitin.
Ya kara cewa karnukan sun kai hari ga ‘yan ta’addan, mace da namiji, wanda hakan ya tursasa su dana bam din a jikinsu. Isah yace karnukan mallakar hukumar CJTF ne.
We appreciate you for reading Teeloadeders, but we think it will be better you like our facebook fanpage and also follow us on twitter below.