Hare-haren Boko Haram na neman sake kazanta a 'yan
kwanakin nan
Kungiyar Dattawan jihar Borno ta Najeriya da ta
kunshi tsoffin sojoji da fararen hula, ta bukaci
gwamnatin kasar da ta yi zaman sulhu da mayakan
Boko Haram da zimmar kawo karshen zub da jini na
tsawon shekaru takwas.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, Kungiyar Dattawan ta
Kanuri ta ce, a can baya, gwamnatin Najeriya ta samu
nasara a tattaunar sulhun da ta yi da mayakan Niger
Delta, abin da ya sa ta ke ganin gwamnatin za ta iya
samun nasara a tattaunawa da Boko Haram.
Kungiyar ta ce, lokaci ya yi da ya kamata mayakan Boko
Haram su ajiye makamanta, sannan kuma su tuba daga
ayyukansu don ci gaba da rayuwa a cikin jama’a.
Kawo yanzu dai, babu wata alama da ke nuna cewa,
gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na shirin
tattaunawar sulhu da mayakan.
Kazalika hare-haren Boko Haram na neman sake kazanta
a ‘yan kwanakin nan tun bayan tafiyar shugaba Buhari
birnin London don duba lafiyarsa, domin ko a jiya Litinin
sai da mutane akalla 8 suka rasa rayukansu a wani kunar
bakin wake a Masallacin Maiduguri.
Shugaban Chadi Idris Deby ya ce, rashin lafiyar
Buhari ta haifar mu su da cikas a yakin da su ke yi da
Boko Haram.
We appreciate you for reading Teeloadeders, but we think it will be better you like our facebook fanpage and also follow us on twitter below.
Title :
Dattawan Borno sun bukaci sulhu da BokoHaram
Description : Hare-haren Boko Haram na neman sake kazanta a 'yan kwanakin nan Kungiyar Dattawan jihar Borno ta Najeriya da ta kunshi tsof...
Rating :
5